Ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu babban matsayi a tarihi kan gaskiya, ƙima da kuma shugabanci na gari.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya bi ayarin ƴan uwa da abokan arziki na Buhari wajen bikin cikarsa shekara 80 da haihuwa, a Abuja.
Ya ce za a tuna da shugaban kamar Charles de Gaulle na Faransa da Winston Churchill na Biritaniya da kuma Franklin Roosevelt na Amurka idan ya bar mulki.
Tinubu ya ce Buhari ya yi tasiri a tarihin Nijeriya a hankali a hankali suna da salon shugabanci na musamman da babu son kai, sadaukarwa da kuma biyan bukatun jama’a.
“Ka karɓi mulki a mawuyacin hali a tarihin Najeriya. Mun ga rayuwar sadaukarwa, kishin kasa da gaskiya. Ka taka rawar gani sosai.
“Al’ummarmu ta ga bambanci. Irin salon jagoranci da ka nuna a lokacin da ka ke karanta jawabin da ka yi a lokacin bikin rantsar da kai a lokacin da ka ke cewa ba ka da dala ko fam, kuma ko da ka na da shi ma to ba za ka bayar dan a zaɓe ka ba.
“Kai mutum ne mai gaskiya, kwazo da tawali’u na musamman,” in ji Tinubu