Daga cikin raunukan da iyaye ko masu raino kan yi wa ƙananan yara ba tare da an sani ba akwai raunin gwiwar hannu da ake cewa “Pulled elbow” ko kuma “Nursemaid elbow” a turance.
Raunin “Pulled elbow” ‘yar ƙaramar gocewar ƙashi ce a gaɓar gwiwar hannu da ta fi samun ƙananan yara ‘yan ƙasa da shekara shida. Raunin na faruwa ne sakamakon saɓulewar ko yagewar tantanin “annular ligament” da ke riƙe da kan ƙashin “radius” a gaɓar gwiwar hannu.
Me ke kawo wannan rauni?
Sakamakon gaɓoɓin yara ‘yan ƙasa da shekara shida ba su gama yin ƙwari sosai ba, saboda haka, tantanin da ke riƙe da kan ƙashin na “radius” bai gama ɗaure ƙashin tamau ba. Wannan ya sa ƙananan yara aka fi jefa wa cikin haɗarin gamuwa da wannan rauni yayin ɗaukansu.
Saboda haka, wannan rauni yana da alaƙa da rashin lura ko ganganci yayin ɗaukan ƙananan yara kamar:
Riƙe tafin hannu ko tsintsiyar hannun yaro tare da ɗagawa da hannu ɗaya ko hannu biyu yayin:
i. goyawa a baya.
ii. yi wa yara lilon hannu.
iii. ɗagawa domin ɗorawa ko saukewa daga abin-hawa, ko kuma tsallakar da su rami ko tudu.
iv. Fisgo hannun yaro yayin wasanni, da dai sauransu.
Domin kauce wa yi wa yara wannan rauni, a zaɓi riƙewa ko ɗaga yara ta hanyar riƙe damatsansu ko kuma sanya hannu tare da riƙo su ta hammata.
Alamun wannan rauni:
1) Yaron da ya samu wannan rauni ya kan yi ƙorafin ciwo daga gwiwar hannu zuwa tsintsiyar hannu musamman idan aka yi yunƙurin motsa hannun.
2) Haka nan, yaro zai maƙale hannun a jikinsa, sannan ya miƙar da gwiwar hannun tare da juya tafin hannun zuwa jikinsa.
Sai dai, irin wannan rauni ba kasafai ya ke zuwa da kumburi a gwiwar hannun ba.
Saboda da hake ne ake kira ga iyaye da masu raino da su guji ɗaga ko ɗaukar yara musamman ‘yan ƙasa da shekara shida ta hanyoyin da aka ambata a sama, sannan iyaye su nusar da masu rainon yaransu domin kiyaye afkuwar wannan rauni.