Mai girma mai dakin dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC Her Excellency Hajiya Hauwa’u A A Zaura ta raba tallafin kayyakin kayan abinci ga iyayen da mazajensu suka rasu suka bar musu marayu a yau juma’a 23/12/2022 a ofishin Hisbah dake karamar hukumar Nassarawa.
Da take jawabi amadadin mai girma Her Excellency Hajiya Hauwa A A Zaura Hajiya Binta Rabiu Zaura ta bayyana tallafin a wani bangare na jin kai da tausayawa irin na Hajiya Hauwa’u A A Zaura kuma ta tabbatar da cigaba da irin wadannan ayyukan alkhairin idan Zaura ya sami dama, Binta Rabiu Zaura ta kara da cewa tallafawa marayu da masu karamin karfi shine abinda zamu mayar da hankali idan Allah ya bamu gwamnati.
Daruruwan Marayu ne suka amfana da wannan tallafi, Mai girma Dagacin kawaji Mallam Abdulkaadir Dan Taura, shugaban J.T.I Alh Nura Gwagwarwa, shugaban kasuwar sabon gari Alh. Bala na daga cikin mutanen da suka halarci taron rabon tallafin