Hukumar Hana Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa NDLEA ta sami nasarar cika hannu da wani Dan kasuwa mai suna Molokwu Nwachukwu, yayin da yake kokarin safarar wata Hodar Iblis pakiti 36 a cikin kayayyakin sa.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Femi Baba Femi shine ya bayyana hakan inda yace an kama hodar ne a lokacin da jami’an hukumar su suke tsaka da binciken kayan matafjya a tashar giragen sama na Lagos.
NDLEA tace mutumin na kan hayar zuwa kasashen China, Dubai, Pakistan da kuma Vietnam,