Hukumar dake yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta ce shigar mata, musamman masu aure cikin harkokin shaye-shaye na daga cikin manyan kalubale da take fuskanta wajen gudanar da ayyukanta a jihar Kano.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da masu ruwa da tsaki ke ganin ya kamata a yiwa dokar data kafa hukumar garanbawul, domin ta dace da sabbin miyagun kwayoyi na wannan zamani.
Akwai kalubale masu yawa da hukumar ta ce tana fama da su, amma tace ofishinta na shiyyar Kano ya kama kayayyakin sanya maye masu nauyin kilo gram fiye da dubu 8, yayin da Jami’anta suka cafke mutane da ake tuhuma da ta’ammali da miyagun ababen dake sanya maye sama da dubu daya a cikin shekarar nan 2022 da ta shude.
Ka Karanta…
Shugaban kasar China ya mika sakon taya murna ga shugaban Russia Vladimir Putin
Yadda gwamnati Kano ta hada hanu da kasar China domin karya Siminti
China ta zargi kasar Amurka da yada labaran karya
Abubakar Idris Ahmad shine kwamandan ofishin Kano na hukumar ta NDLEA mai yaki da fatauci da shan ababen sanya maye ya yi karin haske dangane da wani sinadarin ruwan kwalba da ake yiwa lakabi da “Akurkura” wadda ya fara zama ruwan dare a watannin bayan a jihar Kano, inda dinbin mutane ke amfani dashi saboda wai ance yana maganin cutuka da dama a jikin dan adam, duk da cewa yakan gusar da hankalin wanda ya yi amfani dashi.
Ya ce “Sakamakon binciken da muka gudanar a dakin gwaje-gwajen mu na kimiyya dake shalkwatar hukumar mu a can Abuja, ya nuna akwai sinadarin tabar wiwi a cikin wannan ruwa na Akurkura. A don haka yanzu hukuncin Akurkura daya dana taba rwiwi, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta ayyana”
La’akari da irin wadannan sabbin ababen sanya maye ne masu kula da lamura ke ganin lokaci ya yi da ya kamata a yi garanbawul ga dokar data kafa hukumar ta NDLEA domin fadadawa da kuma inganta hurumi da ayyukanta.
Mohammed Ali Mashi, wani mai bibiyar ayyukan yaki da shaye-shaye a Najeriya, ya kawo shawarar cewa, ya dace majalisar dokoki ta Najeriya tayi kwaskwarima ga wannan doka ta hukumar NDLEA.
Tuni dai masana da kwararru a fannin tsaro ke harsashen cewa, baya ga matasan dake cikin birane da kauyuka, hatta ‘yan fashin daji da sauran ‘yan tarzoma dake tayar da fitina a sassan Najeriya na amfani da irin wadannan ababen Shaye-Shaye