Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, sun taya juna murnar shiga sabuwar shekarar 2023.
Cikin sakon sa, shugaba Xi ya ce shekarar 2022 ta fita daban, inda a cikin ta aka ci gaba da fuskantar manyan sauye-sauye a harkokin kasa da kasa, yayin da kuma aka fuskanci karin bazuwar annobar COVID-19 a sassan duniya, sai dai duk da haka, alakar Sin da Rasha ta ci gaba da kasancewa cikin yanayin bunkasuwa yadda ya kamata.
Shugaba Xi ya kara da cewa, cikin shekarar da ta gabata, hada-hadar tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Rasha na ci gaba da bunkasa, inda sassan biyu suka samu sabbin nasarori a fannin samar da makamashi, da zuba jari, da kara cudanya da juna da dai sauran su, wanda hakan ya ingiza bunkasar kasashen 2.
A nasa bangare kuwa, shugaba Putin cewa ya yi, a shekarar mai karewa, an karfafa tsarin gudanar da hadin gwiwar kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, kuma hakan ya nuna karfin bunkasa, da ikon shawo kan kalubalolin waje da suke fuskanta.
Shugaba Putin ya ce yana da imanin cewa, ta hanyar hadin gwiwa, kasashen 2 za su yi nasarar daga matsayin hadin gwiwar su zuwa sabon mataki, tare da kawowa al’ummun su dunbin alherai.