Biyo Bayan zargin yada kalaman tada hatsniya daga bangaren jam’iyun siyasa da gidajen talabijin na TVC News da Arise tv keyi hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC ta yanka tarar miliyan biyu ga kowanna gidan talabijin.
NBC ta sanar da tarar ne a wata takarda da shugaban hukumar, Balarabe Ilelah, ya saka wa hanu a jiya Juma’a
Ilelah ya an ci tarar gidajen talabijin din ne bayan bada dama da suka yi ga wasu yan siyasa inda suke sakin baki tare da yin kalaman da ka iya tada hatsaniya a kasa.
Yace gidajen yada labaran na TVC News da Arise tv kowa zai biya tarar miliyan bibiyu a cikin sati biyu daga lokacin da wasikar tarar ta same shi.