Gwamna Badaru Muhammad na jihar Jigawa ya amince da nadin Muhammad Hameem a matsayin sabon sarkin Dutse.
Nadin ya biyo bayan rasuwar tsohon sarkin da ya rasu a satin da ya gabata a Asibitin babban birnin tarayya Abuja
Hameem ya gaji Nuhu Muhammad da ya kwashe shekaru masu yawa akan kujerar sarautar ta Dutse.