Kasar Japan ta shiga halin tsaka Mai wuyan– Shugaban kasar

Tare da faduwar adadin haihuwa da karuwar yawan tsofaffi, Japan na iya zama “kasar kakanni.”

A kasar Japan da ke gabashin Asiya, adadin haihuwa a shekara ya ragu zuwa kasa da dubu 800 a karon farko a shekarar 2022.

Ya zuwa farkon shekarar 2023, kashi 29 na al’ummar Japan mai mutane miliyan 124.77 na da shekaru 65 ne ko sama da haka, kuma kashi 11.6 na tsakanin shekarun 0 da 14.

Japan ita ce kasa ta farko a duniya bisa ga jimillar yawan jama’a masu shekaru 65 zuwa sama.

Ita kuma kasar Italiya na da kashi 24.1 sai Finland mai kashi 23.3.

Firaministan kasar Japan, Kishida Fumio ya sanar da cewa kasar Japan na gab da rasa aiyukanta na zamantakewar al’umma sakamakon raguwar yawan haihuwa kuma a bana za su mai da hankali kan manufofin renon yara.

Hukumar Kula da Yara da Iyali, mai alaka da gwamnatin kasar za ta fara aiki a watan Afrilu.

Kisida ya bayyana cewa suna shirin rubanya kasafin kudin manufofin da suka wajaba daga yanzu zuwa watan Yuni.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments