Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo yace kasar na bukatar shugabanni masu tsananin kishin kasa da kuma daukar matakai masu tsauri wadanda zasu taimaka wajen dawo da kimar ta a idan duniya.
Obasanjo ya bayyana kansa a matsayin mai tsananin kishin Najeriya lokacin da ya tarbi Mohammed Hayatudeen dake neman tsayawa Jam’iyyar PDP takara, ya koka sosai akan yadda kasar ta samu kan ta ayau wajen tabarbarewar tsaro da alaka tsakanin jama’a da kuma rashin jagoranci na gari.
Tsohon shugaban yace abinda Najeriya ke bukata ayau shine shugaba mai tsanani wanda zai dinga daukar matakai masu tsauri kamar mai fama da tabin hankali, yayin da ake bukatar yan kasar da su sadaukar da kan su wajen dawo da ita akan hanya.
Obasanjo ya gabatar da matakai guda 4 da yace ya dace wanda zai jagoranci kasar nan ya samu da suka hada da fahimtar yadda kasar take da hangen nesa da kudirin sadaukar da kai wajen rufe ido a yiwa kasa aiki da kuma daukar matakai masu tsauri ko da jama’ar kasa basa so.
A karshen makon gobe ne ake saran Jam’iyyun Najeriya 18 su gudanar da tarukan kasa domin gudanar da zaben fidda gwani wadanda zasu nemi shugabancin Najeriyar