Kamar yadda aka sani doron kasa yana da koguna da tafkuna da manyan teku-teku a nahiyoyi manya daban-daban, yana sauyawa sannu a hankali bayan wasu dimbin shekaru.
Mutum zai iya fahimtar haka idan ya hada hoton taswirar duniya, inda zai ga yadda kasa ta dare ruwa ya shiga tsakani, wanda hakan ya haifar da nahiyoyi daban-daban da tsibirai.
Wata taswira da masu bincike a kasar Australiya suka fitar ta yi hasashen cewa tekun Pacific zai bace, inda nahiyoyin da ya ratsa za su hade wuri daya a samu wata katafariyar sabuwar nahiya da za a kira ta Amasia, can a bangaren arewacin duniya.
To amma fa wannan abu ba zai faru ba nan da wasu shekaru miliyan 200 ko 300.
Abin da masana kimiyyar na jami’ar Curtin ta Australia da jami’ar Peking ta China suka yi hasashen zai faru shi ne, nahiyar Amurka ta Arewa da ta Kudu za su karkata zuwa yamma, sannan nahiyar Asia za ta nufi gabas.
Nahiyar da take kuryar kudu a duniya wadda kuma ita ce ta fi karancin mutane a cikinta, wato Antarctica za ta nufi nahiyar Amurka ta Kudu wato Latin Amurka.
Ita kuwa nahiyar Afirka ta gefe daya za ta hade da Asiya, sannan ta daya bangaren za ta hade da Turai a samu wata katafariyar nahiya da za a kira ta Amasia.
An wallafa sakamakon wannan bincike ne a mujallar kimiyya ta National Science Review.
Samuwar katafariyar nahiya
Jagoran masu binciken Dr Chuan Huang, daga jami’ar Curtin ya ce, “Sakamakonmu ya nuna mana cewa yadda saman duniya ke sanyi karfin tekuna gaba daya na raguwa.
Sannan kuma Tekun Pacific zai motse, ya ragu sosai ta yadda zai kankance, fiye da Tekun Atalantika da Tekun Indiya wadanda su kuma suke kara girma.
An yi hasashen samun sunan ‘Amasia’ ne inda za a same shi daga hasashen hadewar nahiyar Amurka ta Arewa da ta Kudu wadanda ake kiran hadakarsu biyu America, da nahiyar Asiya.
Katafariyar nahiya ta karshe da aka sani ita ce Pangea, wadda ta dare zuwa wasu nahiyoyin daban, can baya shekaru miliyan 180 da suka gabata.
Wannan nahiya kusan ta hada duniya gaba daya a dunkule, kuma a lokacin tana zagaye ne da wani teku guda daya na duniya baki daya da ake kira Panthalassa.
Masanan sun yi amfani da wata babbar kwamfuta ne inda suka fahimci yadda manya-manyan nahiyoyi ke iya faruwa.
Ta irin wannan nazari ne da suka yi a kwamfuta suka ga cewa tuni ma Tekun Pacific yana tsukewa a duk shekara.
Ko da yake kadan ce tsukewar, amma hakan na nuna cewa zuwa miliyoyin shekaru nan gaba hasashen da suka yi a kan tekun zai iya kasancewa.
Dr Huang ya yi hasashen cewa nahiyar Australia za ta yi karo da Asiya da farko sannan kuma daga karshe ta hade da nahiyoyin Amurka ta Arewa da ta Kudu, bayan Tekun Pacific ya bace.
Wani hasashen na daban A baya ma masu bincike sun taba yin irin wannan hasashe na samun wasu manya-manyan nahiyoyin uku, kafin wannan da wadannan masanan suka yi a yanzu na samun Amasia.
Wadanda aka yi hasashen a wancan lokacin su ne Novopangea da Pangea Ultima da kuma Aurica.