Yanzu haka ana ci gaba da tono Mutanen da girgizar kasa mafi karfi a cikin wannan karni ta hada da su a kasar Turkiyya da Siriya inda aka tono kimanin mutane kusan 1300 da suka hallaka.
A cewar shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, adadin mutanen da suka rasu sakamakon girgizar kasar guda 2, da suka girgiza sassan kudancin kasar da safiyar Litinin din nan, ya kai mutum 912, yayin da wasu sama da 5,000 suka jikkata, kuma mai yiwuwa adadin ya karu yayin da ake ci gaba da zakulo mutane da gine gine suka danne.
Kaza lika ita ma ma’aikatar lafiyar kasar Syria ta ce girgizar kasar da ta auku ta hallaka mutane 371, baya ga wasu 1,089 da suka jikkata.