Nageriya ta kwashe shekaru biyu cikin raunin tattalin arziki : Banki Duniya

Bankin Duniya ya ce Najeriya na cikin wani yanayi mai rauni tun shekaru biyu da suka wuce, lokacin da aka samu tashin farashin mai a karshen shekara 2021.

A wani rahoto da ya yi wa lakabi da ”Macro Poverty Outlook for Nigeria” a turanci wanda Bankin ya fitar a wannan wata na Afrilu, ya bayyana cewa Najeriya ta yi amfani da kashi 96.3 cikin 100 na kudaden shigar da ta samu a 2022, wajen biyan basussuka, wanda shi ne ya kawo aka samu gibin kasafin kudi na yau da kullum, ya kara ta’azzara.

Amma ga kwararre a fanin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati yana ganin abinda Najeriya ta yi ba daidai ba ne, saboda a ka’ida, bai kamata kasa ta saki jikinta ba, ace za ta kwashi kudaden shiga da ta ke samu har kashi 96 cikin 100 tana biyan basussuka da su.

Mikati ya ce yin haka zai kawo wa kasar koma baya, saboda haka yana ganin, gara kasar ta tashi tsaye wajen samo karin kudaden shiga, ko walau ta yi karin haraji a cikin kasa ko kuma ta fadada hanyoyi wajen kara al’kaluman da ake samu akan kudaden kaya da ake shigowa da su.

Mikati ya ce kashi 7.5 ake biya na haraji, saboda haka ya bada shawarar a daga alkaluman daga 7.5 zuwa ko kashi 15 ko 30 saboda a samu karin kudade, amma a cewan Mikati idan an bar lamarin haka, ba karamin tashin hankali ba ne, wata rana za a wayi gari babu kudin, kuma ba za a ba kasa bashi ba idan ba ta da kudi ko da na lamuni ne.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments