Dubun dubatar ‘yan Sudan sun yi gudun hijira don tserewa yaki da rashin tsaron da ƙasar ke fuskanta cikin kwanakin nan.
MDD da sauran kungiyoyin agaji sun yi kiran a kawo musu ɗaukin gaggawa a halin da suke ciki.
Jaridar BBC ta ce yawancin mutanen na guduwa ne zuwa wasu ƙasashe makwaɓta kamar Sudan ta Kudu da Habasha da Chadi da Masar da kuma Djibouti.
A jiya Laraba, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Dr Tedrus Adhanum Gebreyesus da ke halartar taro a Geneva, ya bayyana mummunan halin da Sudan ke ciki, inda ya ce hakan zai sake janyo taɓarɓarewar fannin lafiyar ƙasar da ya kusan durkushewa.