Bayan na fito da tsarin hada lambar NIN da layikan waya an tura min sakuna na barazanar mutuwa.
Ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin na zamani Farfesa Malam Isa Ali Pantami yace sau da yawa yana karbar sakon barazana akan za’a kashe shi bayan da ya kirkiro tsarin da sai kowanna da kasa da yake amfani da waya ya hada bayanan da da layin wayar sa.
Pantami ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter
A cewar sa akwai tarin mutanen da basa goyon bayan tsarin kuma ya karbi sakon barazanar ne daga Gare su.
Pantami ya ci gaba da cewa ‘amma sai na fada wa kai na cewa zan iya sadaukar da rayuwa ta ga kasa ta ta Nageriya’
‘tunda na yi tabbacin cewa babu wata kasa da zata ci gaba a Duniya face ta hanyar sabbin hanyoyin tattalin arziki na zamani in ji shi