Makusantan Buhari Sun Fara Janye Wa Suna Komawa Wurin Tinubu
Kakakin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa wasu daga cikin hadiman shugaba Buharu sun fara janye jiki suna komawa tsagin shugaba mai jiran gado, Bola Tinubu
Shehu ya ayyana irin wannan halayyar da wasu ma’aikatan gwamnatin Buhari ke nuna wa a halin yanzu da, “Ɗabi’ar halittar ɗan adam.
A cewarsa, abu ne da kowa ya sani wannan ɗabi’ar mutane ce amma yadda hadimai ke janye wa suna komawa wurin gwamnati mai jiran gado ya banbanta da wanda ya faru a lokacin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck
Kakakin shugaban kasar ya ce akwai banbanci janye jikin baya da na yanzu saboda Jonathan ya nuna kishin ƙasa ne a wancan lokacin, kamar yadda Punch ta rahoto. Shehu yana cewa.
“Lokacin da Jonathan ya mika wa Buhari mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2015 a Eagle Square, akwai wani abun wulakanci da ya biyo baya.