Hukumomi a kasar Indonesiya sun bayyana cewa akalla mutane 174 ne suka mutu a wani filin wasan kwallon kafa a kasar lokacin da dubban magoya baya suka fusata, suka kutsa kai cikin filin wasan inda ‘yan sanda suka mayar da martani da barkonon tsohuwa lamarin da ya haifar da turmutsitsi.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar a birnin Malang, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane 180, na daya daga cikin bala’o’in da suka yi sanadiyar mutuwar mutane a filin wasanni.
Magoya bayan kungiyar Arema FC a filin wasa na Kanjuruhan sun mamaye filin wasan, bayan da kungiyar tasu ta sha kashi da ci 3-2 a hannun kungiyar da suka ziyarta.
‘Yan sandan wadanda suka bayyana tashin hankalin a matsayin tarzoma, sun ce sun yi kokarin tilastawa magoya baya, said ai sun harba hayaki mai sa hawaye ne bayan an kashe jami’ai biyu.
Yawancin wadanda abin ya shafa an tattake su ne ko kuma aka shake su har lahira, a cewar ‘yan sanda.
Wadanda suka tsira da ransu sun bayyana irin firgicin da ‘yan kallo suka shiga a cikin cunkoson jama’a bayan an harba hayaki mai sa hawaye.
Shugaban kasar Joko Widodo ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wannan musiba, da sake duba lamuran da suka shafi dukkanin wasannin kwallon kafa, sannan ya umarci hukumar kwallon kafar kasar da ta dakatar da dukkan wasannin har sai an kammala inganta tsaro.
Amnesty International ta yi kira da a gudanar da bincike kan dalilin da ya sa aka harba hayaki mai sa hawaye a filin wasan.