Wasu Yan bindiga sun yi awon gaba da wani basarake tare da matar sa

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake a jihar Kwara tare da matarsa da kuma direbansa a ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba. Lamarin ya afku da misalin karfe 4:45 na yamma a Owa-Onire, karamar hukumar Ifelodun, jaridar The Nation ta rahoto. Basaraken da aka sace mai suna AbdulRahman Fabiyi ya kasance Onire na Owa-Onire.

Jaridar PM News ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da faruwa al’amarin.

  Okasanmi ya ce: “Rundunar yan sandan ta samu labari a ranar 1 ga watan Oktoban 2022 cewa wasu tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken Owa Onire wani gari da ke karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, tare da maarsa da direbansa.

“Tawagar yan sanda tare da yan sa-kai da kuma maharba sun shiga yankin bisa umurnin da aka basu na ceto mutanen da kuma kamo miyagun.

“Kokarin tawagar ya yi sanadiyar ceto matar basaraken da aka sake yayin da aka kama mutum biyu da ake zargin suna da hannu a sace sun Bello Abubakar mai shekaru 31 da Bawa Seketri mai shekaru 30 kuma suna taimakawa rundunar a bincikenta.”

A karshe ya kuma bayyana cewa ana nan ana giudanar da bincike domin ceto basaraken da direbansa yayin da aka sada matar da iyalinta

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments