Bayan kwashe kwanaki, ƴan bindiga sun sako kwamishiniyar hukumar ƙidaya ta ƙasa da suka sace a jihar Rivers
An yi awon gaba da Mrs Gloria Izonfuo ne a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da ta ke dawowa daga tafiya
Rundunar ƴan sandan jihar Rivers ta tabbatar da sakin Mrs Gloria, sai dai ba ta bayyana ko an biya kuɗin fansa ba