Rabaran Danjuma Byang, mamba daga manyan malaman kiristanci daga Arewa da suka wakilci tawagar Pentecostal wajen ganawa da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya bayyana kadan daga abubuwan da suka tattauna a kai.
Jairdar Guardian ta ruwaito cewa, malamin ya rubuta wata wasikar nuna nadama a kafar WhatsApp, inda ya fasa kwai kan tattaunawarsu da Tinubu.
An zargi malaman na coci da cike aljihunansu da kudade bayan da suka gana da Bola Ahmad Tinubu.
Byang ya tabbatar da halartar malaman na coci, ya kuma yi bayanin cewa, shugabannin sun ziyarci Tinubu don bayyana masa kokensu kan yadda ya dauko tafiyar siyasarsa.
Na karbi na shan ruwa a hanya Ya bayyana cewa: “Tabbas, na halarci ganawar kuma na rubuta takaitaccen rahoto akai.
Na yi mamakin yadda abin da suke iya karantawa kawai batun na karbi kudin hawa mota ne.”
Malaman kiristancin na ci gaba da sukar yadda Bola Ahmad Tinubu ya dauko tafiyar siyasarsa gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa.