Daga Walid Hari.
Dalibai sama da 700,000 ne suka ci jarrabawar kammala sakandire ta 2022 wadda Hukumar Tsara Jarrabawa ta Kasa NECO.
Gidan talbijin na Channels ya ruwaito, Babban Jami’in Hukumar, Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi lokacin da yake sanar da haka a wani taron manema labarai a Minna.
Ya ce masu ruwa da tsaki da dama sun tantance cewa an samu gagarumar nasara a jarrabawar kammala sakandire da hukumar ta yi a shekarun baya-bayan nan.
Wushishi ya ce a cikin dalibi 1,198,412 da suka rubuta jarrabawar, dalibi 727,864 wato kashi 60.74 ne suka ci jarrabawar da fiye da darasi biyar ciki har da Ingilishi da Lissafi.
Farfesa Ibrahim Wushishi ya shawarci daliban da suka rubuta jarrabawar su duba shafin hukumar NECO don ganin sakamako.