kasar Burkina Faso ta sake afkawa cikin tashin tashinar juyin mulki

Sojoji sun sake yin juyin mulki a kasar Burkina Faso.

Sojoji a Burkina Faso sun hamÉ“arar da shugaban gwamnatin sojan Æ™asar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a yau Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata.

Wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau.

Haka nan sun dakatar da aiki da kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma rusa gwamnati mai-ci.

A watan Janairu ne Kanar Damiba ya mulki bayan ya jagoranci juyin mulki.

Tun da farar safiyar Juma’a aka ji Æ™arar harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasar Burkina Faso da kuma hedikwatar sojojin juyin mulki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato shaidu suna cewa.

Sojoji sun tare manyan hanyoyin da suke babban birnin ƙasar Ouagadougou.

An jibge dakarun tsaro a manyan hanyoyin da ke yankin da fadar shugaban ƙasar da hedikwatar sojojin suke.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments