An yi kira ga alummar unguwar Yakaasai da su kwantar da hankalin su kada su dauki matakin ramuwar gayya sakamakon rikicin daba ya yake wakana a unguwar A kwanakin nan.
Daga Abdulhamid Isa D Z
kiran ya fito ne daga bakin kwamadan vigilante na unguwar Yakasai Bola Abdullahi Ibrahim Age A zantawar sa da wakilin Aksammedia Abdulhamid Isa Durumin Zungura.
Age yace suna daukar matakin da ya dace domin ganin An magance faruwar hakan anan gaba.
Kazalika ya bukaci iyaye da Yan uwan wadanda suka sami raunuka da suyi hakuri kar su dauki zuga da wasu mutane akan abin da ya sami yayan su da Yan uwan su.
Tun da fari ya yaba da kokarin da jamian rundunar Yan sanda na kwalli Dibishin da anti Daba suka nuna a lokacin faruwar rikicin a yammacin jiya Laraba 22/06/2022.
Editor A S Gwammaja