Jini abu ne da za a iya cewa daukacin jikin Dan Adam ya dogara da shi kasancewar shine hanyar da dukkan organs da tissue da tsokokin jikin Dan Adam yake samun iskar Oxygen da nuttirit ta hanyar sa.
Abu ne sananne cewa jikin mutum yana dauke da jijiyoyi masu yawan gaske wanda suke dauke da hanyoyi kanana a cikin su wanda jini yake gudana ta su kuma ta hakane yake sanyaya jikin mutum.
Kamar yadda wakilin Aksammedia Abdulhamid Isa D Z ya zanta da, Dakta Murtala Musa Dagumawa na Asibitin Muhammad Abdullahi Wase a jihar Kano yace ana bukatar kowanna mutum ya kasance mai kula da lafiyar sa ta hanyar sanin yadda jinin sa yake gudana a jikin sa domin yana hawa kuma yana sauka wanda ta hanyar kula da shine zai iya sanin yanayin da yake ciki.
Dakta Dagumawa yace idan jini ya dade yana hawa ba tare da yana sauka ba hakan ka iya haifar da da faruwar wasu cututtuka a jikin Dan Adam kamar ciwon Koda da shanyewar barin jiki da rashin bacci da ciwon zuciya da kuma sauran cutuka.
Ya kara da cewa akwai hanyoyin da ake bi domin kaucewa kamuwa da hawan jin, yace idan mutum yana so ya gujewa kamuwa daga hawan jini dole ne ya kasance mai bawa jikin sa hutu da kuma fita motsa jiki
Kazalika yace dan kaucewa hawan jini ana so mutum ya guji shan giya da shan taba sugari da shan gishiri da kayan dandanon girki masu dauke da sinadarin lijitamet mai yawa da kuma nauukan abinci masu dauke da kitse mai yawa.
Daga kaeshe dakta Dagumawa ya yi kira ga masu dauke da yanayin hawan jini da su kasance maabota bibiyar likitotin su domin kulawa da lafiyar su.
Bayan kammala tattaunawar wakilin mu da Dakta Murtala Musa Dagumawa ya sami zarafin jin ta bakin wani mutum mai suna Jamilu Yusuf dake dauke DA yanayin hawan jini da suga inda yace ta hanyar zuwa Asibiti ne yake samun saukin yanayin da yake fama da shi.