Mun samar da daidaito da zaman lafiya a tsakanin yan kasuwa daga karbar shugabancin kasuwar kofar Wambai: jamilu Yahaya Ibrahim

Kungiyar kasuwar kofar Wambai ta jaddada kudirinta na ci gaba da bijiro da managartan shire – shirye domin inganta kasuwancin alummar kasuwar da bunkasa tattalin arzikin yankasuwa.

Babban sakataren kungiyar kasuwar Alh jamilu Yahaya Ibrahim ne ya bayyana haka a lokacin da yake Karin haske ga manema labarai dangane da nasarorin da shugabancin kungiyar kasuwar ya samu tun daga farkon kama mulkinsa zuwa yanzu.

Jamilu yace kungiyar ta samar da Zaman lafiya tsakanin alummar dake gudanar da kasuwanci da bakin da suke shigowa daga wasu wurare domin yin ciniki da samar da tsaron dukiyoyin alumma da nemowa yankasuwa hanyoyin bunkasa Jari.

Sakataren yace, kungiyar ta kuma shigewa yankasuwa gaba wajen samar musu da rumfuna a kasuwar Dalar Gyada domin ganin sun fadada kasuwancinsu da baiwa wanda bashi da rumfa damar mallakartasa da shigo da tsarin tallafawa masu karamin karfi da marayu a duk lokacin da bukatar Hakan ta taso.

Jamilu ya yi kira ga Gwamnatin jiha da ta tarayya da su tallafawa kungiyoyin yankasuwa dake kasar nan duba da yadda kasuwanci yake neman durkushewa a Najeriya, wanda Hakan zai haifar da rashin ayyukan yi a fadin kasar nan.

Haka zalika, sakataren ya bukaci alummar kasuwar da ci gaba da baiwa kungiyar kasuwar cikakken hadin Kai da goyan bayan da ya dace domin ci gaba da bijiro da managartan shire – shiryen da su habaka kasuwancinsu a kodaushe, wanda yin Hakan zai Kara farfado da tattalin arzikin jihar kano.

Daga Ibrahim sani gama pyramid radio.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments