Daga Walid Hari.
Atletico Madrid ta nuna sha’awar sayen ɗan wasan gaba na Brazil da Liverpool, Roberto Firmino. (Todo Fichajes – in Spanish).
Leicester City na sa rai kan ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Netherlands Donny van de Beek, 25. (Ekrem Konur)
Everton ta soma tattaunawa da ɗan wasan tsakiya a Najeriya, Alex Iwobi kan wata sabuwar kwantiragi. (Football Insider)
Dan wasan tsakiya a Faransa, N’Golo Kante, 31, na son ci gaba da zama a Chelsea duk da alakanta shi da Paris St-Germain. (Le10 Sport – in French).
Brentford na shirin miƙa wa Ivan Toney mai shekara 26 sabon kwantiragi domin janye shi daga rige-rigen da Manchester United, Leeds, Newcastle da West Ham ke yi. (Mirror).