Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Mrs Oluwatayin Sakirat Madein a matsayin babbar Accounting ta kasa,
A wata sanarawa da mai magana da yawun ma’ikatan Kulla da ma’ikatan ta kasa Mohammed Abdullahi Ahmad ya fitar yace Shugaban ya amince da nadine a yau Juma’a 19 ga watan Mayu, wannan shekarar, ta 2023
Yace hakan yasa itama Shugaban ma’ikatan ta kasa ta amince da nadin
A wani bincike da Jaridar Aksam Media ta gudanar ta gano Mrs Oluwatayin Sakirat Madein ita ce mace ta farko da ta zama babbar Accounting ta kasa a Najeriya
An dai haifi Dakta Oluwatayin Sakirat Madein a shekara ta 1965 a Karamar Hukumar Iperu Remo Ikenne dake jihar Ogun, sannan ta yi karatun digirin di-gir-gir a fanin Kidindiga a Jami’ar Walden dake Kasar Amurka.