Cibiyar Wayar Da Kan Al’umma Da Kyaukkyawan Shugabanci Ta Kasa Reshin Jihar Kano ta karrama Mai Girma Sarki Dillalan Kano Ambasada Abdullahi Mustapha Arrows
Karramawar ta gudana ne a ofishinsa dake kofar ruwa filin Hajiya Mariya Sanusi Dantata
Dayake bayyana dalilin Cibiyar na karrama Sarkin Sakatar Cibiyar na kasa Reshen Jihar Kano Sule Hussaini Dawakin Kudu, yace sakamako irin ayyaukan alkari na ciyar da marayu da yi musu kayan daki, idan za a aurar da su, yasa cibiyar ta karrama shi da lambar yabo mai takin Ambassador Of The Year
Shi ma da yake mayar da jawabi a wurin taron Sarki Dillalan Kano Ambasada Abdullahi Mustapha Arrows yace ya jidadin da wannan Cibiyar wace ta hada kwararrun ‘Yanjaridu har ta hango irin ayyaukan alkarin da yake yi wa al’mmar jihar Kano da kasa baki daya