Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da takwaran sa na Labour party Peter Obi sun yi da’awar gabatar da shedu da yawan su ya kai 150 a kokarin su na kalubalentar nasarar Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinibu.
A nasu bangaren Tinibu da kashim shettima suma sunyi ikirarin gabatar wa da kotu shedu 39 da 21 da kuma 25 wadanda zasu tabbatar da nasarar da suka samu.