Yau Talata, ministan tsaron kasar Sin Wei Fenghe halarci taron ministocin tsaron kasashen ASEAN karo na 9 da ke gudana a Cambodiya, ya gana tare da takwaransa na kasar Amurka Lloyd Austin bisa gayyatar da ya yi masa. Bangarorin biyu na ganin cewa, ya kamata sojojin kasashen biyu su yi kokarin tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
Yayin ganawar tasu, Wei Fenghe ya nanata matsayin Sin kan batun yankin Taiwan. Ya ce, batun yankin Taiwan yana da muhimmanci ga muradun kasar Sin, da ma huldar kasashen biyu. Taiwan wani yanki na kasar Sin, kuma batun yankin, harkokin cikin gida na kasar Sin ne, ba wanda ke da ikon tsoma baki a cikinsa.