Kungiyar kwallan kafa ta Manchester united ta sallami dan wasanta na gaba kuma dan kasar Portigal Ronaldo mai shekaru 37 biyo bayan zarginsa da aibata kungiyar da muzanta mahukuntanta dayai a wata tattaunawa dayai a makon daya gabata, acewar kungiyar Ronaldo ya aikata badaidai ba, inda ya kira kungiyar da wajan neman kudi ba wai kulob din wasa ba, kazakika ya kara da cewa baya ganin girman mai horar da kungiyar Erik ten hag sabida shima baya girmama shi.
United din sun fitar da sanarwar soke kwantarakin Ronaldo tare da sallamar sa a wata sanarwa da suka fitar mintina kadan da suka gabata.
Ko menene makowar Ronaldo? Lokaci zai bayyana.