Katafaren kamfanin makamashi na Sinopec na kasar Sin, ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar samar da iskar gas (LNG) na tsawon shekaru 27 da kamfanin QatarEnergy a jiya Litinin.
A matsayinsu na kamfanoni mallakar gwamnatocin Sin da kuma Qatar bi da bi, yarjejeniyar za ta baiwa kamfanin QatarEnergy damar samar da tan miliyan hudu na iskar gas a duk shekara ga kamfanin Sinopec.