Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta fitar da rahoto mai taken “Hali da hasashe kan tattalin arzikin duniya a 2023”, a jiya Laraba 25 ga watan nan, wanda ya nuna cewa, karuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2023 zai ragu daga kimanin kashi 3% a shekarar 2022 zuwa kashi 1.9%.
Rahoton ya ce sakamakon tasirin annobar COVID-19, da rikicin Ukraine, da hauhawar farashin kayayyaki da sauyin yanayi ya haifar, tattalin arzikin duniya ya tabarbare a shekarar 2022, kuma tattalin arzikin duniya zai ci gaba da fuskantar matsin lamba a shekarar 2023.
Baya ga haka, rahoton ya yi hasashen cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai inganta a shekarar 2023. Bisa kyautatuwar manufofin rigakafin annobar, da kuma daukar matakai masu kyau a fannin raya tattalin arziki da gwamnatin kasar Sin ke yi, karuwar tattalin arzikin kasar zai kara habaka a bana, kuma ana sa ran karuwar za ta kai kashi 4.8%.
Haka zalika, rahoton ya yi imanin cewa, domin tunkarar rikice-rikice da dama a duniya, da kuma mayar da duniya kan hanyar neman cimma burin ci gaba mai dorewa na MDD kafin shekarar 2030, ya zama wajibi a karfafa hadin gwiwar kasa da kasa. Kana akwai bukatar kasashen duniya su gaggauta kara kaimi wajen bayar da taimakon kudi, da rage yawan basussuka da dai sauransu ga kasashe masu tasowa