Girgizar kasa mai karfin maki 5.6 ta afku a gundumar Luding dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar China.
Bayan afkuwar girgizar kasan, nan da nan sashen kula da harkokin gaggawa na majalisar gudanarwar kasar, ya ba da jagoranci kan aikin ceto da kuma binciken lamarin .
Ya zuwa yanzu, an riga an kammala aikin ceton gaggawa, kuma babu hasarar rayuka, ko rugujewar gidaje a yankin da ibtilain ya afku,
Kazalika hanyoyi, wutar lantarki, da na sadarwa, da kuma layikan samar da ruwan sha, duk sun dawo yadda ya kamata