MDD ta mayar da yan gudun hijira fiye da 100,000 gida a kasar Habasha

Hukumar kula da masu kaura ta MDD (IOM) ta ce, sama da al’ummar Habasha 100,000 da suka kaura ne suka koma gida daga kasashen waje, cikin watanni 10 na farkon bana.

Tsakanin watan Junairu zuwa Oktoba, hukumar IOM ta yi wa mutane sama da 100,000 masu komawa Habasha rejista, inda mafi yawansu da adadinsu ya kai sama da 71,000 suka fito daga Saudiyya.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahoton da ta fitar ranar Laraba, dangane da shirin tunkarar rikicin Habasha.

A cewar hukumar, adadin mutanen da suka koma gida cikin halin ni ’yasu da masu matsalolin lafiya masu tsanani da ma matsalar kwakwalwa, abun tayar da hankali ne dake zaman kalubale ga hukumomin kasar.

Har ila yau, IOM ta ce rikici a arewacin Habasha ya kara tsananta yanayin masu kauran, bisa la’akari da yadda komawa yankunansu ya zama abu mai wahala.

Bugu da kari, hukumar ta ce kimanin daya bisa ukun wadanda suka koma kasar daga Saudiyya, ’yan asalin yankunan dake fama da rikici ne. (

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments