Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero CFR NOL Ya Jaguranchi Addu a ta Musamman A ya jumma a wadda ita juma a ta karshe a wannan Shekara ta 2022 Damuke Bankwana da ita .
Sarkin yaja Hankalin Alumma kan Sudage da Addu a wajan samun saukin wannan tsadar rayuwa da Halin da kasar nan take ciki dan Samun saukin wannan yanayin da muke ciki , sannan sarkin Yayi kira ga yan siyasa da suye yakin neman zaban su cikin kwanciyar Hankali da janhankalin matasa magoya bayansu dasuye cikin kwanciyar hankali batare da tashin hankalin junansu ba da zunda jini a tsakaninsu da sauran jama a baki daya.
A karshe sarkin Yayi Addu a akan Allah yazaba mana shugabanni Nagari wanda za suzama Alkhairi da kasa da Alumma baki daya . Sarkin yayi addu ar masun zaman lafiya da karuwar Arziki ga jihar kano da kasa Baki Daya.
Daga abubakar balarabe kofar na’sa magatakardar yada labaran masarautar jihar kano