Majalisar Dinkin Duniya tace kasar Sudan na gab da rugujewa ganin yadda ake ci gaba da samun amon wuta da karar fashe fashe a birnin Khartoum, duk da tsawaita tsagaita wutar da bangarorin dake rikicin kasar suka sanar a jiya.
Tuni wannan rikici wanda ya shiga mako na 3 ya tilastawa dubban yan kasar Sudan tserewa zuwa kasashen makota irin su Masar da Chadi da kuma Jamhuriyar Afirka domin samun mafaka.
Akalla mutane sama da 500 aka tabbatar da mutuwar su a wannan rikici da ya barke tun daga ranar 15 ga watan jiya, tsakanin shugaban soji Janar Abdel Fateh al-Burhan da mataimakin sa kuma shugaban jami’an tsaron kai dauki na RSF, Mohammed Hmadan Daglo.
Miliyoyin mazauna birnin Khartum sun makale a cikin gidajen su yayin da suke fama da rashin abinci da kuma ruwan sha, bayan katse wutar lantarki, sai kuma jiragen yakin dake ci gaba da shawagi suna kai hare hare ba kaukautawa.
Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa a Khartoum yace ko a jiya litinin an ga jiragen yaki na shawagi a kudancin birnin, yayin da mayakan Daglo ke kai musu hari da makaman kakkabo jirage.
Kasashen duniya kuma sun mayar da hankali ne wajen kwashe mutanen su da wannan rikici ya ritsa da su, yayin da alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna cewar ya zuwa yanzu an kwashe baki sama da 50,000.
Daliban Najeriya na cikin dubban yan kasashen waje da suke fatar ganin an mayar da su gida tun bayan barkewar rikicin, amma har ya zuwa wannan lokaci babu koda mutum guda da aka mayar gida.
Khartoum a kasar Sudan
Khartoum a kasar Sudan AP – Marwan Ali
Sai dai Babban sakatare a ma’aikatar jinkai ta Najeriya, Dr Nasir Sani Gwarzo yace sun sake fasalin kwashe daliban, kuma yanzu za suyi amfani da tashar Port Sudan ne.
Ya zuwa yanzu iyayen wadannan dalibai na cikin zulumi ganin yadda yakin ke ci gaba da kazancewa, yayin da kasashen duniya suka kasa shawo kan hafsoshin dake rikicin.