Shugaban hukumar zaben ta INEC a jihar Adamawa da aka dakatar, Barrister Hudu Yunusa Ari ya musanta zargin da ake yi cewa ya karbi cin hanci na Naira biliyan biyu don ayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta yi nasara a zaben na gwamnan jihar Adamawa.
Binani dai ita ce ‘yar takarar gwamna ta jam’iyar APC a jihar Adamawa a zaben 2023.
Ta kalubalanci gwamna mai ci ne na jam’iyar PDP Ahmadu Umaru Fintiri wanda a karshe hukumar zaben ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben a wa’adi na biyu.
Hudu ya ce ba ya nadama ko kadan game da matakin da ya dauka na sanar da sakamakon zaben gwamnan da aka yi a jihar ana tsakiyar tattara sakamako.
Barrister Hudu Yunusa wanda rundunar `yan sanda ke nema ya ce doka ce ta ba shi hurumin sanar da sakamakon.
Ya kara da cewa a shirye yake ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke nemansa nan ba da jimawa ba.