Masu Sharhi sun bayyana damuwa dangane da makomar bakin da suka makale a Sudan sakamakon yadda aka fara zargin wasu bakin da zama sojan hayar da ke kama wa bangaren ‘yan tawayen yakin
Wannan ya sa suka fara kiran kungiyar tarayyar Afirka ta hanzarta daukar matakan kawo karshen wannan fada da ke daukar sabon salo a kulliyaumin.
A yadda kasashen duniya ke rige-rigen kwashe mutanensu daga kasar Sudan wata manuniya ce da ke fayyace girman rikicin da kasar ta fada sakamakon yadda al’amura suka ki ci suka ki cinyewa a wannan kazamin fada na tsakanin sojan kasar.
Mai sharhi akan al’amuran yau da kullum, Abdourahaman Alkassoum, ya ce yakin yana daukan sabon salo ko kuma yana kara tabbatuwa sun shiga gadan-gadan yakin basasa, inda kasashen da suke da hali ko kuma suka san ciwon kansu suke kwashe mutanensu ciki har da ma’aikatansu na diflomasiyya daga kasar saboda daidaicewar kasar.
Kalaman da aka ji suna fitowa daga bakin Janar Al-Burhan a baya bayan nan a kafafen yadada labarai wani abu ne da ya kamata gwamnatocin kasashe makwabtan Sudan ko wadanda ke kusa da kasar su dauka da mahimmanci.
Zargin mutanen irin wadanan kasashe da kamawa dakarun FSR ko RSF wata magana ce da bai dace a dauke ta da wasa ba.
Alkassoum ya ce shi shugaban gwamnatin Sudan yana zargin kasashe irin su Chadi, Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da cewa daga can ake tahowa da mayaka da suke taimaka wa bangaren ‘yan tawaye, wannan abu yana da tada hankali matuka.
Ya kara da cewa daruruwan dalibai da ‘yan jamhuriyar Nijar sun kasance suna cikin Sudan, kuma bata yi kokarin fito da su ba illa ‘yan kadan, wadanda suka hada da ma’aikatan ofishin jakadancinta da iyalansu da ta dakko kuma wannan zargi idan ba’a yi a hankali ba zai iya jefa su ‘yan kasarta a cikin hadari da kuma sauran wasu kasashe.
A yadda wasu rahotanni ke kwatanta wannan fada a matsayin wanda wasu manyan kasashe duniya ke da hannu a kaikaice ya zama dole kungiyar tarayyar Afirka ta hau matsayinta na mai fafutikar tabbatar da hadin kan kasashen nahiyar, in ji wani dan siyasa Soumaila Amadou.
Ya kuma fara da tunatar da gwamnatin Nijar halin da wasu ‘yan kasar ke ciki a Sudan
Da yake tarbar jami’an jakadancin Nijer da ke Sudan lokacin da suka isa filin jirgin saman a birnin Yamai a makon jiya ta hanyar wani jirgin Faransa, ministan harakokin waje, Hassoumi Massaoudou ya yi ikirarin cewa zasu kwashe dukkan ‘yan kasar dake fatan dawowa gida sai dai kawo yanzu shiru kake ji a yayin da wasu gomman dalibai ke ta kiraye kiraye a kowace rana ta kafafen sadarwa na zamani dangane da halin tashin hankalin da suke ciki a Khartum