Mayakan Ansaru na cigaba da yin Auratayya ta hanyar tilasta mutane a jihar Kaduna

Gwamnan jihar  Kaduna, Nasuru El-Rufa’i ya yaba da kokarin jamian  sojojin ƙasa da na sama da ƴan sanda da jami’an tattara bayanan sirri da ƴan bijilanti da waɗanda suka taimaka wurin samun nasarar kama Yan taadda tare da kwace bindugu da babura masu yawa a jihar kaduna.

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin da ƴan bindiga suke cin karen su babu babbaka musamman a yankin karamar Hukumar  Birnin Gwari da Chikun da ke jihar.

Sai dai a baya-bayan nan gwamnati ta ce tana samun nasara a kan ƴan bindiga, domin ko a kwanakin baya sai da sojojin sama suka kashe wani ƙasurgumi kuma jagoran ‘yan fashin daji da ke ayyukansa a Jihar Kaduna mai suna Alhaji Shanono tare da yaransa 17.

Sai dai bayanai daga yankunan Birnin Gwari da Giwa kuwa na cewa har yanzu akwai mayaƙan Ansaru da ke ikirarin jihadi kuma suna addabar yankunan inda ko a kwanakin baya sai da aka samu rahoton yadda mayakan na Ansaru ke auren ‘yanmatan yankin

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments