Rundunar ƴan sanda ta kasa reshen jihar Kano, ta sami nasarar cika hanu da wani matashi mai suna Gaddafi Sagir, bisa zargin sa da kashe kishiyar mahaifiyarsa, da ƴar ta mai shekara takwas.
kakakin rundunar ƴan sanda na jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa yace lamarin ya faru ne a ranar Asabar a Fadama Rijiyar Zaki da ke Karamar Hukumar Ungogo bayan da mahaifin matashin ya dawo ya sami matarsa, Rabi Sagir, da ƴar ta ta, wacce yar riƙo ce, Munawwara, kwance jina-jina.
Kyawa yace bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu labarin abin da ya faru, nan take kwamishinan yan sanda na jihar Kano ya aika jami’ai zuwa wajen, inda bayan an kai matar da kuma yarinyar Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ne likita ya tabbatar da rasuwarsu.
An dai kama wanda ake zargin ne a wani kango a kokari da yake na tserewa ya bar gari
A binciken farko da aka gudanar, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na yin kisan inda ya ce ya yi amfani da sukun-direba wajen caccakawa kishiyar babar ta sa a wuya sannan ya shake ‘yarta da ɗankwali har sai da ta daina numfashi.
Da ake tambayar sa dalilin aikata kisan, Gaddafi ya ce ya yi hakan ne sabo da marigayiyar ta takura wa mahaifiyarsa.
“Har ta kai ga mahaifiya ta ta bar gidan ta koma garin mu. Ta kuma hada mahaifi na da mahaifiya ta, ta sanya ya na yi mata wulakanci iri-iri. Ni kuma hakan na ɓata min rai,” in ji matashin.
A cewar sa, rigima ce ta kaure tsakanin sa da marigayiya Rabi da safe, lokacin da ya zo ɗaukar abinci, inda yace shi ne ya ɗauki sukundireba ya caccaka mata a wuya.
Ya ƙara da cewa ita ma Munawwara ɗin ya shake ta ne da dankwalin zani sabo da ta “buga mun taɓarya a ka. Shi ne ita ma na shake ta.”
Ya ce shi ba ya shaye-shaye kawai dai sharrin zuciya ne ya sanya ya aikata wannan ta’asar.