Biyo Bayan cin zarafi da mai dakin shugaban DSS Aisha Yusuf Bichi tayi wa Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyar NNPP Abba kabir Yusif wanda aka fi Sani da Abba Gida-gida a ranar Lahadin da ta gabata, yanzu haka jam’iyar APP ta bukaci da a kama shugaban DSS na kasa wato Yusuf Bichi domin ya fuskanci tuhuma.
Bukatar hakan ya fito ne ta bakin shugaban jam’iyar Uche Nnadi, a wani jawabi da ya rabawa manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Nandi yace cigaban zaman Yusuf Bichi a matsayin shugaban DSS wata babbar hanya ce ta barazana.
Ya kara da cewa bai dace a yi watsi da lamarin cin zarafin da matar shugaban DSS din tayiwa dan takarar gwamna na jam’iyar NNPP ba duba da yadda ake zargin jamian Hukumar ta DSS da wuce gona da iri a wasu jihohin kasar nan.