Mai ɗakin Darakta-Janar na hukumar jami’an tsaron farin kaya, SSS, Aisha Yusuf Bichi, ta bada umarnin a tsare ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ta hana shi hawa jirgi da ga Kano zuwa Abuja.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa dambarwar ta faru ne a kofar shiga ɓangaren matafiya masu alfarma na filin jirgin saman Malam Aminu Kano, yayin da ayarin motocin Abba kabir Yusuf, wanda a ka fi sani da Abba Gida-gida, su ka haifar da cinkoso.
Lamarin ya haifar wa da ayarin motar Aisha Bichi tsaiko, yayin da ta ke shiga ɓangaren domin tashi zuwa Abuja.
Majiyoyi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa lamarin ya fusata Aisha Bichi, inda dogaranta su ka riƙa duka kan mai uwa da wabi da ababen hawa saboda “raina Hajiya”.
Shaidun gani da ido sun ce da ƙurar ta lafa, sai Abba Gida-gida ya je don ya yi mata ƙorafin abinda dogaranta su ka yi, a matsayin ta na ƙawar mai ɗakin sa, inda ta riƙa yi masa balbalin-bala’i, har ta ke cewa ba za ta bari ya yi gwamna a Kano ba.
Daga nan dai, in ji majiyoyi, sai ga ƙarin jami’an tsaron farin kaya sun zo, inda su ka tsare Abba Gida-gida har sai da Aisha Bichi ta shiga jirgi ta tashi zuwa Abuja.
Wasu majiyoyin ma sun ce kafin ta tashi zuwa Abuja, a lokacin da ta ke ta faɗa, Aisha Bichi ta hango wani hadimin Abba Gida-gida, Garba Kilo yana ɗaukar ta a waya, inda ta sa dogaran ta su “harbe shi kuma ba abin da za a yi.”
“Ta ci gaba da faɗa, ta kuma rantse cewa Abba Gida-gida ba zai shiga jirgi ɗaya da ita ba. Haka dai aka ci gaba da tsare Abba har sai da jirgin ya tashi matar Daraktan,” in ji majiyar.