Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL, Ya sake nada wasu sababbi Hakimai guda hudu tareda daga Darajar wasu Hakimansa guda shida.
Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa shine ya bayyana a wani sako da ya rabawa manema labarai
Da yake jawabi lokacin da aka nada Hakiman, Mai Martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace an nadasu Sarautun ne bisa cancantar da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.
Wadanda aka nada din sunbhadar da Alhaji Nura Sunusi a Matsayin Dan Darman Kano da Alhaji Sarki Hamidu Bayero a Matsayin Barayan Kano da Alhaji Sayyadi Muhammad Yola a matsayin Fagacin Kano da kuma Alhaji Bello Idi a Matsayin Kaigaman Kano.
Sai kuma Hakiman da aka ciyar dasu gaba sun hada da Malam Umar Sunusi Bunun Kano ya koma Dan Makwayyon Kano da Malam Ibrahim Hamza Bayero Dan Madamin Kano zuwa Dan Ruwatan Kano da Malam Lamido Abubakar Bayero Yariman Kano inda ya zama Bunun Kano.
Saura Hakiman da aka ciyar dasu gaba sune Alhaji Aminu Ahmad Sadiq Zamnan Kano zuwa Dan Madanin Kano da Alhaji Magaji Galadima Kachallan Kano zuwa Magayakin Kano da kuma Alhaji Bello Habibu Dankadai Fagacin Kano zuwa katikan Kano.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR JP, ya bukaci hakiman da aka nada su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tareda gudanar da aikinsu da gaskiya da amana tareda Sanya tsoron.