Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya bayyana cewa yana fama da fuskantar matsin lamba daga sassa daban-daban lamarin da zai iya saka shi ya bar Nageriya
Matsin lambar na zuwa ne a wani martani da yayi jam’iyar APC bayan shan kaye da yayi a takarar sa ta shugaban kasa duk da kiristocin dake fadin Nageriya sun mara masa baya kwansu da karkwata amma ya karkare a na uku
Obi duk da ya fito fili ya karyata rahoton dake yawo na faifen sauti dake cewa zaben da ya gabata kamar yakin addini ne a gurin kiristoci sai dai yace sautin ba muryar sa bace yarfe jam’iyar APC tayi masa