Ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Shoukry ya yi kira da a kawo karshen duk wani nau’in ta’addanci da tsoma bakin kasashen waje a kasar Syria, a kokarin dawo da tsaro da kwanciyar hankali a fadin kasar
Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar ta bayyana cewa, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da manzon musamman na MDD kan kasar Syria Geir Pedersen, babban jami’in diflomasiyyar Masar ya jaddada cikakken goyon bayan da kasar ke baiwa kokarin Pedersen, na cimma daidaiton siyasa a kasar Syria, bisa ga kudurin kwamitin sulhu mai lamba 2254.
A nasa bangare kuwa, wakilin MDD ya godewa Masar bisa gudunmawa da ma goyon bayan da take bayarwa wajen warware rikicin kasar Syria.
A cewar sanarwar, Shoukry da Pedersen sun tattauna hanyoyin rage wahalhalun da al’ummar Syria ke ciki.