Kungiyar masu hada_hadar kasuwancin manja da man gyada dake Bello road kasuwar singa sun sha alwashin siyar da mansu cikin farashi mai sauki duba da alfarmar watan Ramadana da muke ciki da kuma karamar sallah dake tafe.
Shugaban kungiyar yankasuwar manja da man gyadar Alh.Fatiyu iliyasu ne,ya sha alwashin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kasuwar singa dake nan kano.
Yace,kamata yayi yankasuwa su yi amfani da wannan lokaci na azimin domin saukakawa alumma farashin kayayyakin masarufi da sauran kayayyakin bukata da alumma suke bukatar siya,inda yace,shi yasa yankungiyar siyar da manja da man gyadar suka ga dacewar sanar da alumma,sun rage farashin kudin manja da man gyada domin darajar Azimin watan ramadana.
Fatiyu iliyasu,ya kwashe shekaru ashirin da biyu yana sana,ar kasuwancin manja da man gyada,ya bayyana cewa, ya samu nasarori da dama a wannan sana,a da kuma, koyawa matasa kasuwanci tare da yayesu domin cin gashin Kansu.
A don haka ya bukaci alumma da sauran masu bukatar manja da man gyada da su garzaya bello road domin Neman samu sauki da garabasa saboda falalar watan azimin Ramadan da kuma, karamar sallah dake tafe duba da halin matsin rayuwa da alumma suke ciki a yanzu.
Shugaban ya shawarci yankasuwa dake siyar da kayan masarufi musamman a wannan watan azimin Ramadan da su kasance masu tausayawa alumma wajen mu,amullar kasuwancinsu,inda yace,yin hakan zai karawa kasuwacinsu albarka.
Yace, wannan lokaci ne, na Neman lada da samun falalar Allah mahalicci da Neman Allah ya sanyawa harkokin kasuwanci albarka.
Haka zalika,yayi kira ga matasa da su kasance masu Neman sanaoin dogaro da kawunansu da kaucewa raina kananan sana,oi domin daga karamar sana,ace take zama babba, har a ci moriyarta yadda ya kamata.
Ya jaddada cewa, matasa suna da rawar takawa wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban alumma idon har suka zamto alumma ta gari a koina suka tsinci Kansu a ciki.
Fatiyu iliyasu, ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta tallafawa kananan yankasuwa da matasa da basu da sana,a wajen Samar musu da ayyukan da za su dogara da kawunansu domin kaucewa shiga munanan dabiu da basu kamata ba.
Daga karshe yace kofarsu a bude taka ga duk wadanda suke bukatar siyan manja ko man gyada daga nesa ko kusa tun daga kananan hukumomi zuwa jihohi kasar nan baki daya.
Ibrahim sani gama pyramid.