A ci gaba da bayyana damuwa da Magabata ke yi game da halin da kasar ke ciki, tsohon Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi (ii) ya ce lalacewar Najeriya sai ma abin da ya yi gaba.
Khalifan Tijjaniya na Najeriya , Malam Muhammadu Sanusi Na ll, ya bayyana matukar damuwarsa kan halin ni ‘ya su da Najeriya ta fada ciki a yanzu. Ya ce har MA gwanda lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki daga wurin Shugaba Goodluck Jonathan.
Da yake jawabi a iyau Alhamis a wurin wani taro a birnin Lagos da Gidauniyar Akinjide Adeosun (AAF) ta shirya don bayar da kyaututtuka da kuma jajantawa mutanen da su ka bayar da shugabanci na gari, tsohon Sarki Sanusi ya ce Najeriya ce kadai kasa mai arzikin man fetur da ke kukan fatara a daidai lokacin farashin mai ya yi sama sanadiyyar yakin Rasha da Ukraine. Ya yi takaicin yadda Najeriya ta kasa biyan basukanta duk kuwa da irin kudaden da ta ke samu. Ya ce, “idan akwai wani da bai san cewa a yanzu mu na cikin matukar rudu ba, to ya kamata ya sani.”
Tsohon Sarkin na Kano ya ce ko a 2015 din ma Najeriya na cikin matsala, to amma daga lokacin zuwa yanzu, ta dada abkawa ne cikin matsalar.
“Mun aza mun shiga babbar matsala a 2015, ashe ma matsalar ta 2015 ba komai ba ce kan abin da zai faru 2023. Yanzu mu na fama da ta’addanci, mu na fama da ‘yan bindiga, mu na fama da tsadar rayuwa, mu na fama da sukurkucewar darajar naira, kuma abu mafi muni ma shi ne wadanda ke shugabanci yanzu sun a tsammanin za mu gode masu lokacin da su ka sauka, su na ganin za mu yaba ma su. “ Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito shi ya na fadi.
Mai Martaba tsohon Sarkin ya ce tamkar al’amarin bai ma dami shugabannin ba. Wani abin ma, in ji shi, shi ne yadda ba su ma damu da hadin kan kasar ba. Ya ce wadanda su ka yi shugabanci akasari ba su da wata niyya ta hadin kan kasa. “Shin da wace suffa ka ke so a tuna ka bayan shafe shekaru 8 a matsayin Shugaban kasa, bayan shekaru 8 a matsayin Gwamna, bayan shekaru 8 ka na Minista, bayan shekaru 8 ka na Gwamnan Babban Bankin Najeriya? Yaya ka ke so a tuna ka a tarihi? Duk wannan bai dame sub a.”
Akasarin wadanda ke mulki a yanzu, in ji shi, abin da su ke hange kawai shi ne zabe mai zuwa. Magana ce ta yadda za a ci zabe. Kuma wannan ba shi ne muhimmin abu ba