Yayin da kowane bangare ke kokarin sauke nauyi wajen ganin an samu tsaro a Najeriya, Majalisar Dattawa ta bai wa shugabannin bangaren tsaro wa’adin makwanni hudu su tabbatar an tsaro tsao a kasar ko kuma ta dau mataki na gaba.
Sanata Abdullahi Ibrahim Danbaba wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin yan sanda ya ce dole ce ta sa Majalisar ta gayyato jami’an tsaron domin halin rashin tsaron kasar ya tsorata su kuma suna so su ga an samu sauyi nan ba da jimawa ba.
Ganin cewa an jima ana irin wannan ganawar amma lamarin sai kara rincabewa ya ke yi, ya sa mai fashin baki a al’amuran tsaro Keftin Aliyu Umar Babangida yin tsokaci da kakkausar murya, ya na mai kiran da a gaggauta zage dantse saboda munin al’amarin.
Shi ma mai nazari kan al’amuran tsaro da zamantakewa, Abubakar Aliyu Umar, ya yi jawabi cikin fushi ya na cewa wasu na samun kudi ne da harkar tsaro shi ya sa ma batun shawo kan rashin tsaron ke tafiyar hawainiya duk kuwa da rashe rashen rayukan da ake ta yi.
To saidai Sanata Abdullahi Ibrahim Danbaba ya bada tabbacin cewa a wannan karon akwai alamun za a samu sauyi domin sun gamsu da bayanin jamián tsaron.
Abin jira a gani shi ne irin matakan da jami’an tsaron za su dauka da zai kawo sauyi a lamarin tsaron cikin gaggawa.