Bazan sakkoba har sai Buhari ya sauka: wani matashi da ya hau saman gada a jihar kano

Rahotanni na nuni da cewa yanzu haka jamian kashe gobara a jihar Kano sunyi kokarin kubutar da rayuwar wani matashi a da ya hau wata babbar gada dake kofar nasarawa da nufin nuna kosawar sa da mulkin shugaban kasa muhammadu Buhari.

Matashin an sami gano shine yayin da wani bawan Allah mai suna Malam Musa inda ya hango matashin ya Mike akan gadar kuma bayyi watataba ya sanar da jamian kwanakwana tuni suka garzaya domin cetar rayuwar sa.

Kawo yanzu hukumar kashe gobara ta jihar kano ta tabbatar da faruwar lamarin kuma yace  an sakko da matashin  me suna Hamza Yahya  kuma sun mika shi ga rundunar yan sanda ta jihar kano

Shedun gani da ido sun shaida mana ta yadda akayi yahau wurin inda acewar su sunce yayi amfani da guraren da ake makala tallan kamfanoni ne.

Daga karshe alummar kofar Nasarawa sun bukaci gwamnati da ta cire wuraren na talla domin gudun faruwar irin wannan anan gaba

 

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments